Turai: Matakin dole ga karbar bakin haure
September 9, 2015Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sake jaddada bukatarta ta ganin an dauki matakin bay daya na tilastawa kasashen Tarayyar Turai karbar bakin haure ba kuma tare da takaice adadin mutanen da za su dauka ba.
Shi ma dai Shugaban hukumar zartarwar Tarayyar Turai Jean-Claude Junker ya gabatar da wannan shawara a gaban taron majalisar dokokin Turai inda ya bukaci kasashen kungiyar da su kasafa 'yan gudun hijira dubu 120 da ke yanzu haka a kasar Hangari a tsakaninsu ba tare da bata lokaci ba.
Shugabar Gwamnatin Jamus wadda ta bayyana shawarar da shugaban hukumar zartarwar Tarayyar Turan ya gabatar a gaban majalissar Turan a matsayin wani tsani na farko na aiwatar da wannan shiri, ta ce lokaci ya yi da ya kamata kasashen Turai su fara tunanin daukar matakan bayar da mafaka ga illahirin 'yan gudun hijirar da za su shigo kasashen nasu a duk tsawon lokaci a nan gaba ba wai wadanda suka rigaya suka shigo a halin yanzu kadai ba.