1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai na goyon bayan zanga-zanga a Iran

Lateefa Mustapha Ja'afar MAB
October 5, 2022

Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a Iran biyo bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami'an hizba, al'ummar kasashen Turai na fitowa kan tituna domin nuna goyon baya, yayin da EU ta kudiri aniyar daukar mataki.

https://p.dw.com/p/4HmfW
Zanga-zanga goyon nbayan 'yan Iran a Berlin kan mutuwar AminiHoto: Kay Nietfeld/picture alliance/dpa

Masu gangamin na kasashen Turai na kokarin nuna goyon baya ne ga matan da ke jagorantar zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iran. A wani jawabi da ta yi ga manema labarai, shugabar majalisar Tarayyar Turai Roberta Metsola ta jinjina tare da tunawa da matan da suka rasa rayukansu yayin abin da ta kira neman hakkinsu.

Präsidentin des EU-Parlaments Roberta Metsola
Shugabar majalisar EU Roberta Metsola ta jinjina wa mata masu zanga-zangaHoto: Michele Tantussi/Reuters/dpa/picture alliance

Metsola ta ce: "Muna tare da ku Masah Amini kamar Hadis da Minoo da Ghazaleh da Hananeh da Hayadeh da Mahsa Noka da ma wasu masu tarin yawa, a gwagwarmayarku ga mata da kuma 'yanci.

Mambobin majalisar ta Tarayyar Turai daga jam'iyyu dabam-dabam na nuna nasu goyon bayansu ga zanga-zanga a kasar Iran.  Iratxe Garcia Perez mamba ce a majalisar, ta ce: "Abu ne da ba za a amince da shi ba kwata-kwata a karni na 21, a amince da kisan mata yayin da suke kokarin kare hakkinsu."

Sai dai kwararriya a fannin halayyar dan Adam a jami'ar birnin Paris Farfesa Azadeh Khan da ke zaman 'yar kasashen Faransa da Iran ta nuna goyon baya da baki kadai ba zai isa ba. Ta ce: "Ina ganin ya kamata kungiyar Tarayyar Turai EU ta dauki gagarumin mataki da zai nuna wa mahukuntan Tehran, cewa al'ummar da ke kasashen da ake tafiyar da mulkin dimukuradiyya da gwamnatocinsu na goyon bayan Iraniyawa domin tabbatar da dimukuradiyyya da kuma 'yanci."

Solidarität mit iranischen Frauen l Protest in der Türkei, Istanbul
Matan Istanbul na Turkiyya ma ba a barsu a baya wajen zanga-zanga baHoto: Bulent Kilic/AFP

Wasu irin matakan ladabtar EU za ta dauka kan Iran?

A nasa bangaren babban kantoman kasashen ketare na kungiyar ta Tarayyar Turai Josep Borrell ya nunar da cewa EU za ta yi nazarin duk wasu matakai da ya kamata ta dauka. Kasashen na TUrai na shirin daukar mataki kan Tehran din, inda Jamus da Faransa suka mika bukatun kakaba takunkumi ga mahukuntan a kan matakan da suka hadar da na tafiye-tafiye da kuma hana su taba dukiyoyinsu.

Alice Bah Kuhnke mamba ce a majalisar kungiyar Tarayyar Turan daga kasar Sweden, ta ce a yi taka-tsantsan wajen kakaba wa Tehran din takunkumi ganin cewa na baya ma tasiri kalilan suka yi ga mahukuntan. Ta kara da cewa: " Tilas ne idan za a saka takunkumi kai tsaye a sanya wanda zai shafi hukumomi da wadanda ke da alhakin kisan mutane da tayar da hankula da kuma wadanda ke rike da madafun iko."

EU Debatte Iran  Mahsa Amini  Rede  Josep Borrell
Kantoman harkokin wajen EU Joseph Borell ya halarci muhara kan IranHoto: EU Parlament

Ba dai za a tabbara da takunkumin ba har sai majalaaisar ta tattauna ta amince da shi, Sai dai mambobin majalisar  kungiyar Tarayyar Turai na nuna alamun a shirye suke su tabbatar da ganin an kakabawa Iran din takunkumi.