1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai na neman mafita game da matsalar makamashi

Suleiman Babayo MAB
October 21, 2022

Shugabannin kasashen Turai sun yi muhawara kan batutuwa da suka shafi manufofin ketare tare da amincewa da bin tafarki daya wajen samar da mafita kan matsalar makamashi, sakamkon yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.

https://p.dw.com/p/4IX92
Wasu shugabannin kasashen Turai a taron kolin EUHoto: PIROSCHKA VAN DE WOUW/REUTERS

Lokacin zaman taron, an soki matakin Jamus na neman magance matsalar makamashin wajen yin gaban kanta domin samar wa kanta mafita maimakon tafiya tare domin tsira tare. Babu dai mafita ya zuwa yanzu, amma shugabannin na EU sun amince da aiki tare ta hanyar hada kai wanda suka ce ke zama mafita. Bayan tattaunawa ta tsawon lokaci, an amince da kwantiragi daya domin tabbatar da ganin makamashi bai wuce wani farashi ba.

Brüssel EU Gipfel Olaf Scholz
Olaf Scholz a taron kolin EU a BruxellesHoto: PIROSCHKA VAN DE WOUW/REUTERS

Scholz ya ce zai je kasar Chaina

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce akwai tasiri na ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya. Sannan Olaf Scholz ya bayyana shirin kai ziyarar aiki nan da wata guda zuwa kasar Chaina, inda zai zama shugaban wata kasa na farko daga Turai da zai yi ziyara a kasar tun watan Nuwamba na shekara ta 2019.

Olaf Scholz ya ce"Ina tsammani yana da tasiri a ci gaba da dangantaka tsakanin kasashe. Kamar yadda aka sani na je Japan inda na gana da Fumio Kishida da mambobin gwamnatinsa. Shi ya sa nake shirin tafiya Chaina bayan taron kasashe mafiya karfin tattalin arziki na G20."

Wasu shugabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai sun nuna tasirin ganin tattaunawa da Chaina domin samun fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu da ke da tasiri a fannin tattalin arziki a duniya. Shugabannin sun tabbatar da cewa za su tsaya kan batun kare hakkin dan Adam da dimukaradiyya kan wata hulda da Chaina.

Brüssel EU Gipfel Emmanuel Macron
Emmanuel Macron na neman kare Maldova daga kutsen RashaHoto: PIROSCHKA VAN DE WOUW/REUTERS

Macron na neman kare Maldova daga hari

Kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine na ci gaba da daukan hankalin shugabannin na EU, inda Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana gayyatar shugabar Maldova zuwa birnin Paris domin tabbatar mata da goyon bayan kasarsa bayan kutsen Rasha a Ukraine, inda ake ganin kasar Moldova na cikin inda Rasha ka iya kutsawa.

Tuni aka shirya taron taimakon Maodova, kamar yadda Shugaba Macron ya yi karin haske, inda ya ce: "Mun tsaya kai da fata kan gangamin neman taimako ga Maldova, ganin irin abin da kutsen Rasha a kasar Ukraine ya haifar. A watan Nuwamba mai zuwa mun shirya taro kan goyon bayan Maldova inda aka gayyacin shugabar kasar Maia Sandu zuwa birnin Paris."

Ita dai kungiyar Tarayyar Turai tana duba hanyoyin rage dogaro kan fasahar Chaina, da neman hanyar makashi da za a iya dogaro a kai, ba kamar na Rasha ba, wanda ya zama makami a hannun Shugaba Vladimir Putin da ya kaddamar da kutse kan kasar Ukraine. Wannan na daga cikin abin da Ursula von der Leyen shugabar hukumar gudanarwar kungiyar EU ta jaddada.