Turai na neman sa bakin China a yakin Ukraine
April 6, 2023Talla
Da ranar yau Alhamis din ne dai Emmanuel Macron na Faransa tare da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen za su gana da shugaban na China wanda ke da abota mai karfi da shugaban Rasha Vladimir Putin.
Kasashen yamma dai na ci gaba da matsa wa China domin ganin ta taka rawa wajen kawo zaman lafiya a rikicin Rasha da Ukraine.
A hukumance dai China na zaman 'yar ba ruwana a yakin, sai dai kuma wasu na zargin rashin fitowarta ta yi tir da afka wa Ukraine da Rasha ta yi.
A baya-bayan nan ma dai shugaban na China ya ziyarci Rasha tare da tabbatar da goyon bayansa ga Putin, ba kuma tare da ya taba yin magana da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ko da sau guda ba.