1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na fuskantar barazana daga Turai

Ramatu Garba Baba
February 2, 2022

Takaddama a tsakanin fadar Kremlin da kasashen duniya na kara zafi inda yanzu Kungiyar EU ta sake barazanar sanya wa Rasha takunkumi muddun ta kai wa Ukraine hari.

https://p.dw.com/p/46QIP
Russland | PK | Treffen Putin und Orban in Moskau
Hoto: Yuri Kochetkov/AP Photo/picture alliance

Kungiyar tarayyar Turai ta ce; a shirye ta ke ta azawa Rasha takunkumin karya tattalin arziki, muddun gwamnatin Kremlin ta kuskura ta kai wa Ukraine hari ko wata mamaya. Rasha dai, ta ci gaba da musanta zargin yin mamayar a maimakon hakan ma, ta zargi kasashen yamma da kokarin jefa kasarsa yaki da Ukraine.

A 'yan makonnin da suka gabata, an gano yadda Rasha ta tura da dakarunta kusan dubu dari da wasu karin kayayyakin yaki zuwa iyakarta da Ukraine, daya daga cikin dalilan da ya saka kasashen yamma zargin Rasha da shirin mamayan. Batun ya haifar da tsamin dangantaka a tsakanin Rasha da sauran manyan kasashen duniya da kawunansu ke rabe kan rikicin mamayan Ukraine.