1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai: Sake daukar matakan dakile corona

Binta Aliyu Zurmi
October 14, 2020

Gwamnatoci da dama a nahiyar Turai na shirin sake shiga matakin da suka dauka a baya domin yaki da cutar corona ganin yadda nahiyar ke samun yawaitar sabbin kamuwa da cutar a baya-bayan nan. 

https://p.dw.com/p/3juL4
Spanien Madrid | Coronavirus
Hoto: Gabriel Bouys/AFP/Getty Images

A sanarwar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fidda, ta ce akwai sama da mutum dubu dari bakwai da aka samu da cutar a tsukin sati guda. Lamarin da ya karu zuwa ga kaso 34 cikin 100 daga makon jiya da ya gabata.

kasashen Birtaniya da Faransa da Spain suke da mafi yawan sabbin adadin, har wayau hukumar ta ce an samu karuwar masu mutuwa a sanadiyar wannan cutar ta sarkewar numfashi.

Yanzu haka dai Italiya da Faransa da ke jerin kasashen da cutar ta yi wa barna sosai tun bayan isarta nahiyar a karon farko, yanzu sun kai ga matakin rufe wasu wuraren cin abinci da mashaya.

Likitoci sun ce da yawan sabbin kamuwa da cutar a wannan karon matasa ne da basa nuna alamun kamuwa da cutar wanda hakan ya sa suke fargabar barnan da za ta yi idan ta kama tsofi.