Turai ta fita daga sha'anin kasar Yukren
December 15, 2013A wata sanarwa da kwamishin fadada Kungiyar Tarayyar Turai Stefan Fuele ya bayar, ta nunar da cewa baki dayan mambobin kungiyar 28, sun dakatar da duk wata tattaunawa da kasar Yukren har sai shugaba Victor Yanukovych, ya bada cikakken hadin kai da kuma niyya dake nuni da cewar a shirye yake ya cimma yarjejeniya da kungiyar.
Akalla masu zanga-zanga dubu 200 ne suke ci gaba da yin dafifi a dandalin 'yanci na birnin Kiev, suna masu nuna adawarsu da kokarin da gwamnatinsu ke yi na sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da kasar Rasha, maimakon Kungiyar Tarayyar Turai.
Kasar Yukren din dai na neman shiga halin rikici tsahon sama da makwanni biyu, tun bayan da shugaba Victor Yanukovych, ya ki sanya hannu kan yarjejeniya da Kungiyar Tarayyar Turai.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh