Turai ta ja kunnen Iran kan yarjejeniyar nukiliya
July 14, 2019Kasashen Jamus da Faransa da Britaniya sun ja hankalin gwamnatin Tehran kan ta guji duk wani mataki na sabawa yarjejeniyar nukiliyar da suka kulla. Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa IAEA dai, ta tabbatar da cewa Iran ta inganta makamashinta na uranium fiye da yadda yarjejeniyar nukiliya ta amince mata na sama da kaso uku a shekara ta 2015.
A share guda kuma, wata majiya a Amirka ta ce, ministan harkokin wajen kasar Iran Javad Zarif ya sami izinin shiga Amirka don halatar taron Majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a birnin New York a wannan makon mai kamawa.
Majiyar ta kara da cewa, matakin bai wa babban jami'in na Iran visar shiga kasar, ya nuna cewa Amirka ba ta da niyyar mayar da Iran saniyar ware duk da tankiyar da ke a tsakaninsu kan shirin nukiliya.