Turai ta kakaba takunkumin sayen ɗanyen mai daga Iran
January 23, 2012Shugabannin ƙasashaen Turai sun cimma yarjejeriyar sanya takunkumi kan kwangilan shiga, ciniki ko sufurin ɗanyan man Iran, a wani mataki na matsin lamba wa ƙasar kan shirin nukiliyarta, ta hanyar rufe hanyoyin samun kudaden shigarta. To sai dai dangane da gudun kara tarwatsa tattalin arzikin turan, wanda a yanzu haka ke cikin halin kaka nika yi saboda matsalar basussuka, gwamnatocin turan sun amince da aiwatar da wannan takunkumi daga mataki zuwa mataki. Hakan zai bawa ƙasashen da ke da kwangila da Iran ɗin, damar zartarwa daga yanzu zuwa watan yuli. A taron su a birnin Brussels ɗin kasar Belgium, ministocin harkokin wajen Turai, sun kuma amince da hana babban bankin Iran ɗin taɓa kaddarorinsa dake ketare, tare da haramta gudanar da duk cinikin zinare da wasu muhimman hajoji da bankin a ɓangaren masana'antu da hukumomin gwamnati. Wannan yarjejeniya da gwamnatocin Turan suka cimma a yau, wanda ya ke zuwa daidai da na Amurka, na da nufin tilasta wa Iran tsayar da shirin makamashin nukiliyarta, wanda Amurka da ƙasashen Turan ke zargin makaman ƙare dangi ne.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdullahi Tanko Bala