1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai zata tallafawa binciken maganin Covid-19

Zainab Mohammed Abubakar
May 3, 2020

Shugabannin kasashen Turai sun amince da shirin tara kudi Euro biliyan bakwai da rabi, domin shawo kan annobar Corona.

https://p.dw.com/p/3biWr
Brüssel | EU Gipfeltreffen: Angela Merkel, Emmanuel Macron und Usula von der Leyen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Matthys

Shugabar hukumar gudanarwar Turai Ursula von der Leyen ta ce, kudin na bangaren kokarin da duniya ke yi na samo allurar riga-kafi da maganin Covid-19.

A gobe Litinin ne za a gudanar da taron tara wadannan makuddan kudaden ta yanar gizo, domin cike gibin karancin kudin da binciken maganin Coronan ke fuskanta.

Wannan shiri ya samu goyon bayan fraministan Italiya Giuseppe Conte, da shugaba Emmanuel Macron na faransa, da kuma takwararsa ta  Jamus Angela Merkel, a wata budaddiyyar wasika da jaridu suka wallafa a yau Lahadi.

Bugu da kari shugaban majalisar Turai Charles Michel da fraministan Norway Erna Solb, su ma sun rattaba hannu tare da bada goyon bayansu ga hukumar kula da lafiya ta duniya, bayan da Amurka ta soki hukumar da zarginta da yiwa annobar "rikon sakainar kashi".