1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai tana nazarin sanyawa Iran ƙarin takunkumi

December 1, 2011

A yayin da Iran ke ci gaba da yin fito-na-fito da ƙasashen yammacin duniya akan shirin niukiliyar ta, Turai na shirin sanya mata ƙarin takunkumi

https://p.dw.com/p/13KKK
Kantomar kula da manufofin ƙetare a tarayyar Turai Catherine AshtonHoto: AP

A wannan Alhamis ce ministocin kula da harkokin wajen ƙasashen dake cikin ƙungiyar tarayyar Turai za su gudanar da taro a birnin Brussels, fadar gwamnatin ƙasar Beljiam domin duba irin takunkumin da za su ƙara sanyawa Iran bisa shirin niukiliyar ta. A baya bayannan ne dai hukumar kula da harlkokin makamashi a duniya ta fitar da wani rahoton dake nuna alamun cewar Iran na yin ƙoƙarin samar da makaman niukiliya.

Akwai dai yiwuwar sanyawa wasu jami'ai da kuma kamfanonin ƙasar ta Iran jerin takunkumin hana tafiye-tafiye da kuma na haramta musu taɓa kadarorin su dake ƙetare, amma sanyawa ƙasar takunkumin karya tattalin arziƙi, abu ne da sai an cimma dai dai to akan sa.

Duk da taƙaddamar dake ƙara zafafa a tsakanin Iran da sauran ƙasashen yammacin duniya sakamakon harin da wasu ɗalibai a ƙasar suka kaiwa ofishin jakadancin Birtaniya dake Iran, ministan kula da harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ya ce wannan baya daga cikin dalilan kiran taron.

A halin da ake ciki dai Birtaniya ta rufe ofishin jakadancin ta dake birnin Tehran sakamakon harin, kana ƙasashen Jamus da Faransa da kuma wasu ƙasashen sun janye wasu daga cikin jami'an diflomasiyyar su daga ƙasar ta Iran na wucin gadi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu