1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai za ta karfafa dangantakar cinikayya da Afirka

Binta Aliyu Zurmi RGB
March 10, 2020

Kungiyar EU ta gabatar da sabon shirin shiga nahiyar Afirka a wani mataki na neman kulla alakar cinikayya tsakanin nahiyoyin biyu duk da sabanin ra'ayoyi da ake samu.

https://p.dw.com/p/3ZAxa
Äthiopien Ursula von der Leyen  Addis Ababa
Hoto: Reuters/T. Negeri

A watan Fabarairu ne shugabar hukumar Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula Von der Leyen ta jagoranci tawagar kungiyar zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha inda ake da hedkwatar Kungiyar Tarayyar Afirka, a zaman taron aka tattauna sabbin matakai na hadin gwiwa. Batu na farko shi ne samar da mafita a kan matsalar sauyin yanayi dama fasahar sadarwar zamani.
 

Batun masu neman mafaka a nahiyar Turai, wanda aka dade ana sukar lamirin Kungiyar EU na hana bakin haure daga nahiyar Afirka shiga Turai na daga cikin batutuwan da za a mayar da hankali a kai, amma tuni wakilan kungiyar suka kare kansu daga wannan zargi.

Gidauniyar Menschen für Menschen mai taimakon al'umma da ke Jamus na mai ganin akwai bukatar a sasauta al'amura don kar tarihi ya maimaita kansa.

Wani batu da ake kuma son ganin kungiyar ta mayar da hankali a kai, shi ne inganta rayuwar al'umar nahiyar ta Afirka musamman ma matasa da akasarinsu ke zaman kashe wando a sakamakon rashin aikin yi, ana ganin cewa su ne suka fi yawa a cikin al'umma akwai bukatar a tallafa musu don rage bara gurbi da ake kallo na asassa tashe-tashen hankula a sassan nahiyar.