Turai za ta kewaye wa takunkumin Amirka kan Iran
May 17, 2018Kasashen Turai sun sanar da daukar matakin kewaye wa duk wani takunkumin tattalin arziki da kasar Amirka ke shirin saka wa Iran domin ci gaba da yin huldar cinikayya da ita.
Matakin wanda kasashen na Turai suka dauka a taron da suka gudanar a birnin Sofia, ya tanadi soma amfani da wata ayar doka mai suna "Blocking Status" wacce suka kirkira a shekara ta 1996 domin kewaye wa takunkumin tattalin arzikin da Amirka ta saka wa Kuba. Wannan doka ce kasashen na Turai suka kwaskware domin samun hurumin ci gaba da huldar kasuwancin da kasar ta Iran ba tare da fuskantar tarnaki a gaban kotu ba.
Takunkuman tattalin arzikin da kasar Amirka ke shirin saka wa Iran bayan ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar da kasashen duniya suka cimma da kasar ta Iran a shekara ta 2015, za su haramta wa kamfanonin kasashen Turan duk wata huldar cinikayya da kasar Iran, lamarin da kuma ke iya kasancewa wata babbar asara ga kasashen na Turai da dama, a daidai lokacin da kasashen Rasha da China suka fara shirye-shiryen maye gurbin kamfanonin Amirka da na Turan wadanda matakin takunkumin zai tilasta wa dakatar da huldar cinikayya da kasar ta Iran.