Rasha: Katse makamashin gas ga Turai
August 19, 2022A cikin wata sanarwar da ya fitar kamfanin Gazprom ya ce aikin gyaran bututun zai shafe tsawon kwanaki uku, kana za a samu raguwar makamashi kamar yadda aka saba da kasa da Cub-miter miliyan 33 a rana, lamarin da zai kara haddasa karancinsa a Turai a daidai lokacin da ake tsaka da bukatar makamashi. Sabon matakin na gwamnatin Rasha ya kara zafafa muhawarar da ta karade nahiyar Turai na zargin ko Rasha na amfani ne da makamashi a matsayin makamin yaki, tun bayan da ta shiga takun saka da manyan kasashen Yamma da suka nuna adawa da mamayar da take yi wa Ukraine. Duk da takun sakar da ke tsakaninta da Turai, Rasha na samarwa nahiyar kaso 40 cikin 100 na makamashin gas, sai dai a baya-bayan nan yana fuskantar katsewa daga Rasha saboda abin da ta bayyana da gudanar da muhimman aikace-aikace a bututan Nord Stream 1 da ke dakonsa zuwa Turan.