Turkiya ta kaddamar da hare-hare kan IS da PKK
July 27, 2015Talla
Kasar Turkiya ta kaddamar da farmaki da jiragen saman yaki kan 'yan tawayen Kurdanawa na kungiyar PKK. Haka ya zama gagarumin farmaki tun shekara ta 2011. Akwai tsoron matakin zai iya jefa shirin zaman lafiya tsakanin kasar ta Turkiya da kungiyar PKK cikin hadari. Matakin gwamnatin ya biyo bayan hallaka wasu sojoji biyu cikin yankin Kurdawa.
Tuni Turkiya ta kira taron kungiyar tsaro ta NATO-OTAN bayan hare-haren da ta kaddamar da PKK da kuma kungiyar IS a Siriya, amma kasar ta kawar da yuwuwar tura dakarun kasa domin yaki da IS a Siriya.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nemi Firaminista Ahmet Davutoglu ya ci gaba datattaunawa da al'umar Kurdawa.