1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Aan ci gaba da farautar dan bindiga

January 2, 2017

Hukumomin Turkiyya sun kaddamar da gagarumin bincike domin gano dan bindigar da ya kai hari gidan rawa a Santanbul wanda ya hallaka mutane 39 da jikkata wasu da dama.

https://p.dw.com/p/2V7po
Türkei Istanbul - Polizei sichert Nachtclub nach Angriff
Hoto: Reuters/O. Orsal

'Yan sanda a Turkiyya sun kaddamar da gagarumar farautar dan bindigar da ya hallaka mutane 39 galibinsu fararen hula a wani harin kan mai uwa da wabi ga masu bikin sabuwar shekara a birnin Istanbul.

Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ya ce an nufi haddasa rudani da tashin hankali ne a wannan hari yana mai cewa kasar ba za ta bada kai bori ya hau ga dukkan wata barazana ba.

Gwamnan Santanbul Vasip Sahin ya ce sai da maharin ya fara harbe wani dan sanda da kuma wani farar hula a kofar gidan rawar kafin ya bude wuta kan mai uwa da wabi a kan masu liyafar sabuwar shekara a cikin gidan rawar wadanda aka kiyasta cewa sun haura mutane 600.
      
A halin da ake ciki hukumomi a kasar sun hana yada labarai game da harin bisa dalilai da suka kira na tsaro da kauce wa tada hankalin al’umma.