1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya na hakar iskar gas tekun Bahar Rum

Binta Aliyu Zurmi
December 20, 2020

Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ta fidda sanarwa ci gaba da ayyukan hakar makamashin iskar gas a gabashin tekum Bahar Rum, duk da rikicin da ake yi tsakaninta da kasashen Girka da na Cyprus.

https://p.dw.com/p/3myzL
EU warnt die Türkei vor Gasförderung vor Zyperns Küste
Hoto: AFP/TURKISH DEFENCE MINISTRY

Wannan dai na zuwa ne bayan sanarwar da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi a wata tataunawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na cewar Turkiya na da burin daidaita dangantakarta da kungiyar EU.


Shugaba Erdogan har yanzu yana kan bakansa na nuna cewar yankin da ake wannan aikin mallakar kasar sa ce kuma bai ga laifi a ayyukan da suke yi ba.


Kungiyar ta EU ta yi barazanar kakabawa Turkiyya takunkumi a game da wannan aiki na hakar iskar gas sai dai mahukuntan na Ankara ba su nuna alamun janyewa ba.