Turkiyya na muradin zuba jari a Afirka
June 2, 2016Da farko dai ganawar Erdogan da Yuweri Museveni ta kafa tarihi, domin shi ne karon farko da wani shugaban kasar Turkiyya ke kai ziyara a Yuganda. Sai dai akwai masu cewa bawai ga huldar kasuwanci kawai ke zama sabon abu ba, amma daukin dangantakar Turkiyya da kasashen Afirka wani sabon babi ne. A cewar Dr. Chritian Johannes Henrich, shugaban wata cibiyar nazarin al'amuran kudancin Turai da yankin Kaukasus.
"Turkiyya ta fara nuna kwadayinta a Afirka tun shekara ta 1998, tun wancan lokacin akwai jadawalin kutsuwa Afirka a bangaren Turkkiya, sai dai ba'a samu aiwatar da jadawalin bisa matsalar ciki da wanda Turkiyya ta fuskanta. Kowa yasan cewa kasashen Afirka na kudu da Sahara sun samu habakar tattalin arziki ta kashi biyar cikin dari, hakan kuwa ya nuna tattalin arzikin Afirka abune mai mahimmanci. A shekarata 2005 Turkiyya ta sake farfado da wannan jadawalin, sai dai akwai abinda ke kumshe a wannan manufa ta Turkiyya. Inda ta fara karfafa hulda kasashen Afirka masu bin akidar sunna, kasashen Yuganda na daga ciki, inda kashi 12 cikin dare na 'yan kasar mabiyan Sunni ne"
Inda batun akidar addini tafi fitowa fila cikin manufar Erdogan dai shi ne, yadda tun shekaru yake kara kusantar kasar Somaliya. Kamar yadda jagoran kidauniyar Henchrich Böll a Istanbul ya bayyana.
"Somaliya klasace ko wane lokaci Erdogan ke zumudin ya shiga, kuma fili take akwai akidar addini a ciki. Abu guda Turkiyya ke fada shi ne, mu zamu iya yin fiye da abinda kasashen yamma suke yi. Misa mu zamu yi muku mahimmanci a matsayin abokanen hulda abinda Erdogan ya fada kenan yayin ziyararsa a Somaliya. Kasashen yamma sun bari kun tarwatse, a yanzu Turkiya na nuna musu abinda yaka mata. Yanzu muna niya yawo cikin wannan kasar, domin mu musulmai ne, don haka mune muka fi fahimtar kasarku"
A dai-dai lokacin da Turkiya ke kara nausawa zuwa Afirka, kamata ya yi abi hanyar da dokokin kasa da kasa suka shinfida, kamar yadda jami'in ya yi karin haske.
"Turkiya bawai tanan bukatar sayar da hajojinta ya fi damunta, a gani wannan ba shi ne abinda zai fadawa Moseveni ba, kuma Erdogan ba zai fada cewa 'yan jaridan Yuganda sun yi nasa yancin gudanar da aiki ba"
A yanzu yada kasashen Burazil, Indiya da China suke kara samun baza komarsu a Afirka, sannu a hankali ita ma Turkiya abinda take neman kafawa kenan.