1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita kan jigilar abinci daga Ukraine

July 21, 2023

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na ci gaba da rarrashin takwaransa na Rasha Vladimir Putin kan yerjejeniyar fitar da abinci daga Ukraine wacce wa'adinta ya kawo karshe a Litinin din da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4UEgn
Hoto: Sputnik/Xinhua/IMAGO

A yayin wani taron manema labarai da ya yi bayan dawowarsa daga ran gadin da ya kai wasu kasashen Gabas ta Tsakkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce yana kyautata fatan samun amincewar shugaba Putin domin dorewa da yerjejeniyar mai matukar mahinmaci domin kaucewa fargabar hauwawar farashin kayan abinci musanman a kasashe matalauta.

Sai dai shugaba Erdogan ya bukaci kasashen Yamma da su sake duba sharuddan da Rasha ta gindaya na dauke mata takunkuman da suka makara mata kan kayan da take fitarwa ta tekun Bahar al Asuwad.

Moscow dai ta ce muddin ana son dorewa da yerjejeniyar wacce aka rattaba a karon farko a watan Yulin bara bisa jagoranci Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya sai an ba ta dama kamar Ukraine domin fitar da wadansu kaya ciki har da sinadaren hada takin zamani.