Turkiyya na son bude iyaka ga 'yan gudun hijira
February 28, 2020Talla
Mai Magana da Yawun Jam'iyya mai mulkin Turkiyya ta AKP Omer Celik ne ya sanar da haka a ranar Jumma'a. Wannan sabuwar matsaya ta kasar Turkiyya ta zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa 'yan gudun hijira 300 ciki har da mata da kananan yara na kan hanyarsu ta shiga kasar Girka ta bangaren iyakar Turkiyya da ke Arewa maso Yamma.
Sai dai jim kadan da fitar da wannan matsaya ta Turkiyya, Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD ta ce ba ta samu wani labari a hukumance dangane da yunkurin Turkiyya na sauya manufofinta a kan 'yan gudun hijirar Siriya ba, kuma ba ta samu rahoton wasu 'yan gudun hijira da ke kan hanyarsu ta zuwa kasar Girka ko wata kasa a tarayyar Turai ba.