Majalisar dokoki na nazarin tura dakarun kasar Libiya
January 2, 2020Talla
Nan gaba a yau din nan ne ake sa ran majalisar zata tafka mahawara a kan batun, kana kuma masu sharhi na cewa jam'iyyar AKP ta shugaba Recep Tayyip Erdogan da kawancenta ta MHP na da adadin 'yan majkalisun da ke iya basu gagarumin rinjayen domin yin n'am da kudrin dokar.
A karshen watan Nuwamban da ya gabata na shekarar bara ne dai shugaba Erdogan, ya cimma wata yarjejeniyar tsaro da gwamnatin kasar Libiya mai goyon bayan MDD karkashin jagorancin Fayez al-Sarraj a wani yunkuri na tallafa mata yakar dakarun sojan da ke biyayya ga Khalifa Haftar mai yunkurin kwace mulki daga gwamnatin kasar.