1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Sake kyautata alaka da wasu kasashe

November 29, 2021

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya za ta sake kulla alaka da kasashen Masar da kuma Isra'ila, kwatankwacin wanda ta yi da Hadaddiyar Daular Larabawa. 

https://p.dw.com/p/43cXF
Türkei I Abu Dhabis Kronprinz Scheich Mohammed bin Zayed al-Nahyan in Ankara
Hoto: Ali Balikci/AA/picture alliance

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Turkiyya da UAE kan wasu batutuwan da suka shafi yankin, sai dai ziyarar da yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Sheikh Mohammad bin Zayed ya kai birnin Ankara a makon da ya gabata ya farfado da dangantakar yayin da kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar zuba jarin biliyoyin daloli.

Erdogan ya ce Turkiyya za ta sake tura jakadunta zuwa kasashen Masar da Isra'ila yayin da yake shirya kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Fabarairun badi.

Tun a shekarar 2013 ne Turkiyya da Masar suka datse alakarsu bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi, wanda ke goyon bayan Erdogan. Yayin da a shekarar 2018 Turkiyya ta kori jakadan Isra'ila a kasarta biyo bayan kisan masu zanga-zanga a zirin Gaza.