Turkiyya ta bukaci mutanenta su rage zuwa Turai
January 29, 2023Talla
Turkiyya ta gargadi 'yan kasarta da su dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen nahiyar Turai, idan har ba su zama dole ba.Turkiyyar ta ce batancin da ake yi wa Qur'ani mai tsarki, na nuna tsangwamar al'adun ketare da Turawa ke yi.
Gargadin na Turkiyya na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da kasashen Denmark da Finland da Norway da Sweden, inda Turkiyya ta ce an wulakanta littafi mai tsarki, suka bukaci mutanen kasashensu da su kaurace wa yin balaguro zuwa Turkiyya.