1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin Turkiyya na cin moriyar yakin Ukraine

Mahmud Yaya Azare SB)(ZMA
March 4, 2022

Matakan da Turkiyya ke dauka dangane da yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, na ci gaba da jawo sharhi daga masu fashin baki kan kokarin da Turkiyya ke yi na ramuwar gayya kan Rasha.

https://p.dw.com/p/481z8
Türkei Istanbul | Präsident Erdogan bei virtuellem NATO Treffen
Hoto: Presidential Press Office/REUTERS

 

Kasar ta Turkiya dai ,da ta jima tana zama kada ran kada han da Rasha, sakamakon kokuwar samun karfi iko da cimma muradunsu a yankin Gabas ta Tsakiya da na Balkan da suke ta yi, ba ta yi wata wata-wata ba wajen amsa rokon shugaban Ukraine na tura mata jiragen yaki marasa matuki, dama toshewa Rasha mashigun ruwanta da za ta iya amfani da su wajen kwaso jiragen ruwan yakinta da makamai da ke jibge a babban sansanin sojinta da ke birnin Torsoun na kasar Siriya.

Karin Bayani:Rayukan fararen hula na salwanta a Ukraine

Sai dai kasar ta Turkiyya a hannu guda ba ta daina ayyana kanta a matsayin mai son shiga tsakani don sasanta kasar ta Rasha da kasashen na Yamma ba, lamarin da Dr Wanis Abdul-azeez masanin kimiyyar siyasa a cibiyar binciken lamuran Gabas ta Tsakiya na kasar Jodan ke dauka a matsayin wani yunkurin jifan tsuntsu biyu da dutse daya da Turkiyya ke yi:

Symbolbild I Serbien I Militär
Hoto: Gregor Mayer/dpa/picture-alliance

"Yakin da ke wakana a Ukraine ya tilastawa Turkiyya daukar sabuwar dabarar ganin wannan yakin da ake bai kai ga shiga halin haihuwar guzuma uwa kwance ya kwance a yankin ba. Don haka,duk da kokarin da take na huce haushinta kan Rasha,kan irin kashe sojinta dama hanata yin sakat da tayi a Siriya,gami da gogayya da ita a Libiya."

Ya kara da cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya na ci gaba da karfafa iko tsakanin kasashen duniya.

Shi kuwa Dr Khalid Gabralawy kwarraren kan dabaru da falsafar yaki da ke Faransa a ganin sa kasar ta Turkiyya a matsayin mamba a kungiyar tsaro ta NATO, wacca kuma take zama a matsayin ganuwa ga kasashen Yamma daga duk wata barazanar tsaron da za ta iya tunkararsu daga gabas, za ta yi amfani da wannan yanayin yakin da ake ciki a yankin, wajen karawa kanta damara da sake yin lale kan wuraren da za ta baza ikonta na soji a yankin.