Turkiyya ta fice daga cikin Istanbul Convention
July 1, 2021Kasar Turkiyya ta fice daga cikin yarjejeniyar da ita da wasu kasashen Turai suka kulla kan kare mata daga duk wasu na'uka na cin zarafi. Yarjejeniyar da aka yi ma lakabi da Istanbul Convention, ganin an cimma matsaya tare da rattaba hannun kan yarjejeniyar a birnin Istanbul na kasar Turkiyyar, ta soma fuskantar kalubale, bayan da Turkiyyan ta ce, ta gano, wasu daga cikin hakkokin mata da ake hakilon karewa ya sabawa al'adu da addinin Musulunci, dalilin da ya sa ta fice daga ciki a hukumance a wannan Alhamis.
Daruruwan mata da kungiyoyi masu rajin kare hakkokin mata da masu mu'amalar jinsi guda ne suka tarbi matakin da zanga-zangar nuna adawa, amma kamar yadda Shugaba Erdoghan ya fadi, kafin ma shiga yarjejeniyar, Turkiya na da tsarin kare hakkin mata da hana cin zarafinsu, amma duk wata mu'amala ta jinsi kamar madigo haramun ne ga al'adun kasar.