Erdogan: Mun shirya kai hari Siriya
October 8, 2019Talla
Da ya ke tsokaci kan wanna mataki, Shugaba Erdogan ya ce "Lokaci ya yi da zamu share hanyar wanzuwar zaman lafiya. Za mu iya kai farmaki a kowane lokaci. Za mu kaddamar da harin ta sama da ta kasa. Muna da yakinin samun goyon bayan kawayenmu da ke Siriya."
Sama da wata guda kenan Shugaba Erdogang ke barazanar kai samamen soja kan mayakan Kurdawa a arewacin Siriya. Matakin na Turkiyya na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Amirka ke janyewa daga bakin daga a Arewa maso Gabashin kasar Siriya. Matakin da ke shan suka daga kawayen Siriya da sauran kasashen duniya.