1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya za ta samu karin kudin tallafa wa 'yan gudun hijira

Mohammad Nasiru Awal USU
March 14, 2018

Hukumar kungiyar tarayar Turai ta EU ta ba da shawara kasashe membobinta su ware Euro miliyan dubu biyu daga kasafin kudinsu don ba da gudunmawa ga Turkiyya.

https://p.dw.com/p/2uJHv
Türkei EU Flüchtlingsdeal Symbolbild
Hoto: picture alliance/abaca/Depo Photos

Kasar Turkiyya za ta samu karin Euro miliyan dubu uku don tallafa wa 'yan gudun hijira da ta ba wa mafaka. Hukumar kungiyar tarayar Turai ta EU ta ba da shawara kasashe membobinta su ware Euro miliyan dubu biyu daga kasafin kudin kasashensu don ba da gudunmawar, yayin da kungiyar za ta ba da sauran Euro miliyan dubu daya.

Sai dai wasu kasashe kamar Jamus da Faransa na masu ra'ayin cewa kamata ya yi kungiyar ta ba da kudaden gaba daya daga cikin kasafinta.

A karkashin yarjejeniyar shekara ta 2016 kan tallafa wa 'yan gudun hijira, aka amince da tallafa wa Turkiyyar wadda ta karbi bakoncin miliyoyin 'yan gudun hijira musamman daga kasar Siriya.

Kungiyar EU na shirin mayar da 'yan gudun hijirar da suka shiga tsibiran kasar Girika ba bisa ka'ida ba, zuwa kasar Turkiyya.

Tuni dai kasar ta yi amfani da kashin farko na Euro miliyan dubu uku da aka ba ta. Kawo yanzu ta ba wa 'yan gudun hijira miliyan 3.5 mafaka.