Turkiyya za ta sasanta shugabannin Rasha da Ukraine
March 28, 2022Tuni dai jirgi dauke da wakilan kasar Rasha ya sauka a filin jiragin sama na birnin Santanbul a Turkiyyan, gabanin tattaunawar da za su yi a ranakun Talata da Laraba. Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine, ya nunar da cewa kasarsa za ta iya amincewa da wasu bukatun Rasha da suka hadar da zama 'yar ba ruwanmu da kuma sassauta matsayarta a kan wasu yankuna da ake takaddama a kansu a yankin gabashin kasar tare da tabbatar da tsaro ga Rasha domin samun zaman lafiya ba tare da bata lokaci ba. Zelenskyy ya kara jaddada cewa tattaunawar gaba da gaba tsakanin shugabannin kasashen biyu ce kawai, za ta kawo karshen yakin. Sai dai ministan harkokin waje Rashan Sergey Lavrov ya nunar da cewa, shugabannin kasashen biyu za su iya ganawa ta gaba da gaba ne kawai bayan an cimma wata matsaya a tattaunawar sulhun. Ukraine din dai ta zargi Rasha da amfani da makami mai guba a kan 'yan kasarta, abin kuma da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya magantu a kai yana mai cewa:
"Yin hakan zai haifar da mummunan sakamako. Mun amince da daukar tsattsauran mataki in har hakan ta afku, kuma tuni mun fara tunanin matakin da ya kamata mu dauka. Ba abu ne da zamu tattauna a kansa ba yanzu, amma dai muna aikewa da sako cewa "Kada a yi hakan!"
Sojojin Ukraine dai sun sanar da sake kwace iko da wani karamin kauye da ke birnin Kharkiv, birnin na biyu mafi girma a kasar da dakarun Rasha suka kwace iko da shi a kwanakin baya. An dai kwashe sama da wata guda ana bata kashi tsakanin bangarorin biyu, inda dakarun Rasha suka samu damar kwace iko da wasu yankuna ciki har da birnin Kharkiv. Sai dai rahotanni sun nunar da cewa dakarun Ukraine sun samu damar sake karbe iko da kauyen Malaya Rohan, mai nisan kimanin kilomita biyar daga birnin na Kharkiv. Mahukuntan na Ukraine dai, sun koka kan yiwuwar samun gagarumar matsalar jin kai a kasar, sakamakon hare-haren na Rasha. Tuni ma dai sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa ya bayar da umurni ga shugaban Hukumar Bayar da Agaji ta Duniya, kan su gaggauta ganin yadda za a tsagaita wuta domin kai kayan jin kai ga wadanda ke cikin bukata.
A hannu guda kuma Amirka ta bayyana cewa ba ta da niyyar sauya gwamnati a Rasha ko wata kasa ta daban. Sakataren harkokin wajen Amirkan Antony Blinken ne ya bayyana hakan, a wata hira da ya yi da manema labarai a Lahadin da ta gabata a birnin Kudus yayin wata ziyara da ya kai Isra'ila inda yace:
"Abu mafi sauki shi ne, a daina bai wa Shugaba Vladmir Putin karfin da zai iya ci gaba da yaki. Ko nuna karfi a Ukraine, ko kuma wata kasa ta daban. Ba mu da wani shiri na sauya gwamnati a Rasha ko kuma wata kasa ta daban ma."
Kalaman na Blinken dai na zuwa ne, kwana guda bayan da shugaban Amirkan Joe Biden ya janyo cece-kuce sakamakon wasu kalamai da ya furta yayin ziyararsa a kasar Poland. A jawabin nasa dai, Biden ya ce: "Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ba zai ci gaba da zama kan mulki ba". Koda yake tuni ofishin Shugaba Biden ya fitar da wata sanarwa da ta ce ba a fahimci kalamansa ba ne, inda sanarwar ta kara da cewa Biden na nufin Putin ya daina nuna karfi ko iko ga makwabtansa ko kuma kasashen yankin.)