1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Turkiyya za ta shiga rikici

Mahmud Yaya Azare LMJ
December 11, 2019

Turkiya ta nuna aniyarta na tura dakarunta zuwa Libiya domin kare gwamnatin hadakar kasar da al'ummomin kasa da kasa suka amince ta ita.

https://p.dw.com/p/3UeKq
Türkei l Präsident Recep Tayyip Erdogan spricht vor seiner Abreise zu den NATO-Führungskräften
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip ErdoganHoto: picture alliance/AA/M. Aktas

Matakin na Turkiya na zuwa ne, bayan da a makon da ya gabata ta kulla yarjejeniyar tsaron juna da gwamnatin hadakar Libiyan da kashen duniya suka amince da halaccinta. Shugaban Turkiya Racep Tayyip Erdogan ne dai ya bayyana aniyar kasar tasa, yayin da yake mayar da martini ga sukan yarjejeniyar da kasarsa ta kulla da gwamnatin hadakar ta Libiya karkashin jagorancin Fa'iz Sarraj da kasashen Girka da Masar ke yi yana mai cewa:

Tabbatar da tsaron kan iyakoki

"Idan halastacciyar gwamnatin Libiya ta nemi mu tura dakarun sojojinmu domin tabbatar da tsaro a Tripoli da kewaye daga hare-haren 'yan tawaye, zamu amsa kiran nata domin da ma yarjejeniyar da muka cimma da juna ta tanadi tabbatar da tsaron kasashenmu da cin moriyar arzikin da ke iyakokinmu na kan teku."

Türkei Militär an de Grenze zu Syrien
Turkiyya za ta tura sojojinta LibiyaHoto: Getty Images/B. Kara

Yarjejeniyar dai ta kunshi bai wa juna tsaron iyokin kasashe na kan teku da na kasa. A ranar Talatar da ta gabata ne dai kasashen biyu suka cimma yarjejeniyar tsaron da aiki tare domin hakar arzikin man fetur da iskar gas da ma'aidinai da ke iyakokin kasashen biyu na ruwa.

Wannan furicin nasa dai na zuwa ne, a daidai lokacin da dakarun janar Haftar ke kara nausawa cikin birnin na Tripoli don gama kame shi daga hanun hukumar hadin kan kasar da ke samun halaccin Majalisar Dinkin Duniya. Dama dai mai shiga tsakani na Majalisar ta Dinkin Duniya Gassan Salamah ya yi kashedin cewa, muddin ba'a dauki matakan tsagaita wuta a birnin Tripoli ba, to janar Haftar da ya samu tallafin miyagun makamai da sojojin haya daga kasar Rasha da ake kira da wagner, na dab da kwace birnin, lamarin da ka iya haifar da mummunan kisan kiyashi.

Libyen Wadi Rabea Al-Sunbulah Luftangriff auf Keksfabrik
Kasar Libiya na fama da tashe-tashen hankulaHoto: AFP/M. Turkia

Zargin yi wa yarjejeniya zagon kasa

Tuni dai majalisar dokakin kasar ta Libiya da ke Tripoli, ta bakin kakakinta Al-Sadeeq Al-Kuhaily ta nuna aniyarta ta gayyatar dakarun Turkiyan domin bai wa birnin na Tripoli kariya daga wadanda suka kira da sojojin hayar ketare da ke ayyukan ta'addanci a kasar Libiya. Hakan dai na wakana ne adaidai lokacin da ake shirin shirya wani taro na kasa da kasa a birnin Berlin na Jamus da nufin daukar matakan kar ta kwana domin sasanta bangarorin da ke yakar juna a Libiyan. Yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani domin cimmata a birnin Sukhairat na Maroko shekaru hudun da suka gabata ne dai, ta kai ga kafa gwamnatin ta hadakar karkashin jagorancin Fa'iz Sarraj. Sai dai ana zargin Khalifa Haftar da kasashen da ke mara masa baya wato Masar da Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Faransa da Rasha da yi wa yarjejeniyar zagon kasa.