Amirka: Sabon kalubale ga Trump
January 9, 2021Kafar sadarwar ta Twitter ta bayyana shugaban Amirkan mai barin gado Donald Trump da wani hadari ga shafinta, tana mai cewa bayan karatun ta nutsu da ta yi wa abubuwan da yake wallafawa a shafinsa na @realDonaldTrump, ta yanke shawarar dakatar da shi na din-din-din domin kaucewa ci gaba da yadaa kalaman tunzira.
Matakin na Twitter da ya katse Trump daga masu bin shafin nasa miliyan 88 da dubu 700 dai babban koma baya ne ga shugaban, a daidai lokacin da yake fuskantar babban hargitsi na kwanakin mulkinsa da suka rage, kana yana iya janyo masa babban kalubale idan ya yanke shawarar koma wa fagen siyasa a shekara ta 2024.
Shugaba Trump da ke zaman dan jam'iyyar Republicans mai mulki a Amirkan dai, ya sake nunara da rarrabuwar kai a rubutun karshe da ya wallafa a shafin nasa na Twitter, inda yace ba zai halarci rantsar da abokin hamayyarasa na Democrats Joe Biden da za a yi a ranar 20 ga wannan wata na Janairu da muke ciki ba. Tuni dai Biden din ya mayar da martini yana mai cewa hakan ya yi kyau, inda ya bayyana Trump din a matsayin wani abin kunya ga Amirkawa.