1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Ana kwashe mutane daga Mariupol

May 1, 2022

Hukumomi da kungiyoyi a Ukraine, sun tabbatar da fara kwashe fararen hula da suka makale a yankin Mariupol. sakamakon kawanyar da sojojin Rasha suka yi wa yankin.

https://p.dw.com/p/4Agrm
Ukraine | Krieg | Evakuierung aus Mariupol
Hoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Kungiyar agaji ta Red Cross, ta sanar da kwaso fararen hula a yankin Mariupol na kasar Ukraine, musamman ma wadanda ke a ma'aikatar nan ta sarrafa karafa ta Azovstal da dakarun Rasha suka yi wa tsinke.

Kamar dai yadda rahotanni daga yankin ke tabbatarwa, tuni aka fidda gomman mutanen cikin wasu jerin gwanon manyan motoci na bas-bas.

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, ya ce lallai akwai sama da mutum 100 da aka kwashe daga Mariupol din, kuma suna ci gaba da aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya don ganin an dora.

Rasha dai ta ce akwai akalla mutum 2,500 a yankin, kuma galibin su sojojin Ukraine ne da kuma wasu sojojin haya daga kasashen ketare.

Yankin na Mariupol dai na da babbar tashar jirgin ruwa da sojojin na Rasha suka yi wa kawanya tsawon makonni.