1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harbe-harbe a wani kauyen Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
February 18, 2022

An ji karar harbe-harben bindigogi a wani kauye da ke gabashin Ukraine wanda ke karkashin dakarun gwamnati, duk da tabbacin da Kiev ta bayar cewa: ba ta da niyyar kai hari a kan 'yan aware masu goyon bayan Rasha.

https://p.dw.com/p/47EYH
Grenzgebiet Ukraine-Russland, Donbas | Konflikt zwischen Russland und der Ukraine
Hoto: Yulia Surkova

Wasu ma'aikatan kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, sun ce an ji karar harbe-harben ne daga Stanytsia Luganska. Wannan sabon tashin hankalin ya zo ne a daidai lokacin da takun-saka tsakanin kasashen Yamma da Rasha ke karuwa, sakamakon fargabar mamayar Rasha a Ukraine din. Sai dai a wannan Jumma'ar ministan tsaron Ukraine ya sake nanata cewa sojojinsu ba su da niyyar kai farmaki kan 'yan awaren. A nata bangaren dai, Rasha ta zargi Kiev da shirya kai farmaki kan yankin Crimea da ta mamaye. Su kuwa kasashen Amirka da Birtaniya sun zargi Rashan ne da neman madogara wajen mamaye Ukraine, lamarin da Moscow ta musanta. Sannan Kremlin ta nuna damuwa dangane da barkewar tashin hankali a gabashin Ukraine.