1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Hare-haren Rasha a birnin Kiev

Abdullahi Tanko Bala
November 15, 2022

Rasha ta kai hare haren makamai masu linzami a Kiev babban birnin Ukraine da wasu gine gine a wasu biranen kasar da suka hada da tashar wutar lantarki

https://p.dw.com/p/4JZkg
Ukraine Kieg mit Russland Raketen auf Kiew
Hoto: Oleksandr Gusev/REUTERS

Shugabannin kungiyar kasashe masu ci gaban masana'antu na duniya G20 suna shirin baiyana damuwa da tabarbarewar yanayin bashi a kasashe masu matsakaicin tattalin arziki.

Daftarin kudirin shugabannin na G20 wanda kamfanin dillancin labaran Reuters ya gani ya maida hankali a kan batun bashi wanda shugabannin suka ce yana barazana musamman ga kasashe matalauta.

Taron ya kuma mayar da hankali sosai kan yakin Rasha da Ukraine inda yawancin shugabannin da suka halarci taron suka yi tir da matakin Rasha a Ukraine.

A jawabinsa tun da farko yayin bude taron kolin, shugaban kasar Indonesia kuma mai masaukin baki Joko Widodo ya yi kira ga kasashen su kawo karshen yakin.

Shugaban Amirka Joe Biden da na Jamus Olaf Scholz da na Faransa Emmanuel Macron da Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da sauran shugabanni suka halarci taron.