1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Jam'iyyar mai ci ta lashe zabe 'yan majalisa

Ramatu Garba Baba GAT
July 22, 2019

Jam'iyyar sabon shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ta lashe akasarin kujeru a zaben 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a karshen mako.

https://p.dw.com/p/3MXhc
Ukraine Präsidentschaftskandidat Selenskyj in Paris
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Lebedeva

 Jam'iyyar sabon Shugaba Volodymyr Zelensky, ta samu gagarumin rinjaye da kashi 43.9 ciki dari na adadin kuri'un da aka kada. Kuma tun bayan da hukumar zabe ta soma bayyana sakamakon zaben ne, magoya bayan jam'iyyar ta Shugaba Zelensky suka soma murna bayyana farin cikinsu ganin yadda sakamakon ya zo daidai da fatan al'umma. A jawabinsa na farko bayan sanarwar, dan wasan barkwancin da ya rikide zuwa dan siyasa ya kuma jadadda alkawuran da ya yi na ganin bayan rikicin da ya daidaita kasar:

"Wannan ba alkawari ba ne kadai, nauyi ne a kaina da sauran tawagata, za mu cika alkawuranmu, babban burinmu ina sake nanatawa, shi ne mu kawo karshen yakin nan da kuma yin nasara kan matsalar cin hanci da ya yi wa kasar katutu".

Jama'a da dama sun yaba da tabbacin da Shugaban ya kara ba su, cike da fatan alheri gareshi da 'yan majalisun da za su yi wannan tafiya tare. Rostislav Lyutov dalibi ne da ya ce faduwa ce ta zo daidai da zama:

''Ina matukar farin ciki da wannan sakamako, don jam'iyya mai ci ta shugaban da muke so ce ta samu rinjaye, a taikace zan ce sakamakon da al'ummar kasar Ukraine baki daya ke fatan gani kenan''

Ukraine | Präsidentschaftswahlen | Reaktion Wolodymyr Selenskyj
Hoto: picture-alliance/dpa/ZUMA Wire/S. Glovny

Shakka babu ra'ayoyi sun sha ban-ban, duk da cewa jam'iyyar Zelenskiy ta sha alwashin gudanar da sha'anin mulki ba tare da wata hadaka ba, wanda shi ne karon farko da jam'iyya guda za ta yi hakan tun bayan da kasar ta sami 'yanci kanta 1991. Wasu na ganin tafiya ce mai cike da kalubale, Oleksandr Habelko wani dan kasuwa a kasar da ya ce abin da kaman wuya:

"Ban ji dadin sakamakon ba, ni ban fahinci muradun wannan jam'iyyar ta Servant of the People ba, kama daga wadanda suka kafa ta ya zuwa magoya bayanta, sai dai kuma ina farinciki sabuwar majalisar na da fatan bin tsarin diflomasiya ta EU''

Ukraine Schauspieler Volodymyr Zelensky
Hoto: picture-alliance/Pacific Press/A. Gusev

Wasu kuwa sun yi marhabin da sakamakon ne cike da fatan ganin an sami sauyi a kasar kamar yadda Olena Moskalenko wata mai sharhi kan lamurran da suka shafi tattalin arziki a kasar ta fadi, yana da kyau a rufe tsohon babi a bude wani sabo.

Jam'iyyar adawa ta 'yan aware ita ta zo ta biyu a yayin da jam'iyyar tsohon shugaban kasar Petro Poroshenko ta zo ta uku. Har wa yau, kasuwannin hannayen jari suma sun yi marhabin da wannan nasara ganin yadda kudin kasar ta Ukraine ya sami tagomashi a karon  farko a sama da shekara guda.