Ukraine na fama da karancin makamashi
November 26, 2022Shiyoyi 15 na kasar Ukraine ne a yanzu ke fama da karancin ruwan sha sakamakon yadda Rasha ke tsananta hare-hare a kan tashohin samar da wutar lantarki da dama na kasar.
Kamfanin samar da makamashin lantarkin Ukrenergo, ya ce rabin yankunan kasar ne kadai yake iya sama wa wutar.
Har i zuwa jiya Juma'a ma dai ko a Kyiv babban birnin kasar ma dai, rabin gidaje ne suka samu wuta.
Sai dai ofishin magajin garin birnin, ya ce kashi biyu bisa uku na samun makamashin dumama gidaje a wannan lokaci na tsananin sanyi na hunturu.
Haka ma a cewar hukumomin an shawo kan matsalar karancin ruwa a Kyiv din da ke fadar gwamnatin kasar.
Hukumar Lafiya ta Duniya dai na gargadin cewa hare-haren na Rasha a kan cibiyoyin samar da makamashi na iya zama babbar barazana ga rayuwar 'yan Ukraine din.