Ukraine na son Jamus ta matsa wa Rasha lamba
January 8, 2015Firaminstan kasar Ukraine ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a yau Alhamis, inda ya nanata bukatarsa ta ganin ta kara kafewa kan batun ci gaban takunkumin karya tattalin arziki ga kasar Rasha, a yayin taron tattaunawa kan rikicin Ukraine da shugaba Vladimir Putin a mako mai kamawa.
Arseniy Yatsenyuk na ziyarar zuwa wannan babbar kasa cikin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai mai mambobi 28 gabanin sake matsaya kan shirin karya tattalin arzikin kasar ta Rasha wacce tuni abin ke shafar dukkanin bangarorin biyu.
Jawaban da ke fiitowa daga bangaren makusantan shugaba Merkel da shugaba Francois Hollande na Faransa na nuni da cewa, mahukuntan biyu na duba watanni biyu na abubuwan da suka faru kan rikicin na Ukraine inda za su duba yiwuwar yin sassauci ko akasin haka kan kasar ta Rasha.