1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na zargin Rasha da hallaka fursoninta na yaki

January 25, 2024

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya yi kiran a gudanar da binciken kasa-da-kasa kan hatsarin jirgin saman sojin Rasha a iyakar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4bgft
Jirgin sama na sojin Rasha da ya yi hatsari a Belgorod
Jirgin sama na sojin Rasha da ya yi hatsari a BelgorodHoto: TASS/dpa/picture alliance

Rasha ta ce kimanin fursononin yaki na Ukraine 65 na cikin jirgin a lokacin da ya yi hatsari a iyakar yankin Belgorod.

Shugaba Zelensky ya jaddada bukatar a gudanar da bincike kan musabbabbin hatsarin inda ya zargi Rasha da yin wasa da rayukan fursononin kasarsa.

An bukaci ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba da ya samar da dukannin bayanan da Ukraine ta samu ga kawayenta.

Yayin da Ukraine ke neman a gudanar da bincike, Rasha ta zargi Ukraine da kakkabo jirgin a lokacin da yake wucewa ta Belgorod.

A ranar Laraba ce dai gwamnan yankin ya ce babu wanda ya tsira da ransa a hatsarin.