SiyasaTurai
Shugaba Putin na Rasha zai yi waya da Biden na Amirka
December 30, 2021Talla
Shugaba Joe Biden na Amirka da Vladimir Putin na Rasha na shirin tattaunawa a kan tasirin jibge dakarun da Rasha ke yi a kusa da iyakarta da Ukraine. Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov ya siffanta tattaunawar da cewa alamu ne na dattako da Shugaba Vladimir Putin ke nunawa a siyasar duniya.
''Shugaba Putin ne ya assasa tattaunawar, kuma manufa ita ce mu ci gaba da tattaunawa kan batutuwa masu sarkakiyar da ba mu tsayar da matsaya a kansu ba a tattaunawarmu ta karshe.'' inji Peskov
Sai dai Fadar gwamnatin Amirka ta White House ta ce Shugaba Biden zai yi amfani da tattaunawar tasu ta wayar salula wurin jan hankalin Rasha a game da dakaru kusan 100,000 da ta jibge kusa da iyakarta da Ukraine.