Dakarun Rasha na dosawa birnin Kyiv na Ukraine
March 11, 2022Rasha ta kara fadada hare-harenta na soji a kan Ukraine a wannan Jumma'a. Na baya-bayan nan shi ne amfani da jiragen yakin da take yi kusa da filin jiragen sama a yammacin Ukraine a karon farko. Kazalika hotunan tauraron dan Adam sun nuna yadda dakarun Rasha ke kara dosawa birnin Kyiv, fadar mulkin Ukraine, bayan kwashe sama da mako biyu suna hankoron shiga birnin.
Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba Vladimir Putin ya amince da shirin dakarunsa na daukar sojojin sa-kai daga ketare da za su taimaka musu ci gaba da yaki a Ukraine. Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ce kawo yanzu mutane sama da 16,000 ne ke neman Rasha ta dauke su aikin soja, galibinsu kuma daga kasashen Larabawa.
Sai dai kuma MDD ta ce kawo yanzu mutum miliyan biyu da rabi ne ya gudu daga Ukraine don kauce wa tashin hankali.