1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Amfani da makami mai linzami kan Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
March 19, 2022

A yayin da aka shiga mako na hudu a ci gaba da gwabza yaki a Ukraine, Rasha ta yi amfani da makami mai linzami samfarin "hypersonique" kan Ukraine a karon farko tun bayan gwajin makamin a shekarar 2018.

https://p.dw.com/p/48jFp
Yakin Ukraine- Birnin Kiev
Hoto: Alex Chan Tsz Yuk/Sopa/Zuma/picture alliance

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta yi amfani da makami mai linzamin da ke cin dogon zango "hypersonique" wanda ta yi wa lakabi da "Kinjal" don lalata wani katafaren sansanin ajiye makamai mallakar dakarun sojan Ukraine a yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Rasha Ria Novosti, ya ambato ma'aikatar tsaron Rasha na cewa makamin da ke layan zana, ka iya kaucewa duk wasu matakai na kakkabo makamai masu linzami a sararin samaniya.

Mosko dai ta ce wannan ne karon farko da ta yi amfani da makamin mai kyaftawa da Bismillah a rikicinta da kasar Ukraine da ya shiga mako na hudu, tun bayan gwajin makamin da kasar ta yi a shekarar 2018.