1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Amirka ta gargadi mutanenta kan zuwa Rasha

March 30, 2022

Sojojin Ukraine sun ce suna da shakku a sanarwar da Rasha ta yi a ranar Talata cewa za ta janye dakarunta daga biranen Kyiv da Chernihiv da suka yi wa kawanya. 

https://p.dw.com/p/49D3T
Russland Wladimir Putin
Hoto: Attila Kisbenedek/AFP

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta sake nanata gargadi ga Amurkawa da kada su yi gigin zuwa kasar Rasha. Sabon gargadin na Talatar da ta gabata, ya ce da-gangan jami'an tsaron Rasha za su iya fito da dan kasar Amirka su illata shi a wani mataki na 'huce takaici' daga manyan matakan ladabtarwar da Amirka ke dauka a kan mahukuntan Moscow biyo bayan mamayar da suka yi wa Ukraine.

Wannan na zuwa ne a yayin da jakadan Ukraine Sergiy Kyslytsa ya shaida wa Kwamitin Sulhu na MDD cewa kawo yanzu Rasha ta yi asarar sojoji sama da 17,000 tare da wasu daruruwan tankokin yaki da suka subuce mata biyo bayan tirjiyar da mutanen Ukraine ke yi wa kutsen da fadar Kremlin ta yi.