Jamus na son a Rasha ta janye dakarunta daga Ukraine
September 13, 2022Talla
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a yayin tattaunawarsu ta waya da takwaransa na Rasha Vladimir Poutin ta tsawon mintoci 90, ya bukaci Rasha da ta dakatar da buda wuta, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya nuna cikakkiyar fata na ganin an samu masalaha ga rikicin Ukraine.
Gwamnatin Jamus ta kuma bukaci Rasha da ta cigaba da mutunta yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine da aka cimma karkashin jagorancin Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya.