Ukraine ta bankado badakalar kudin makamai
January 28, 2024Talla
Tuni dai aka kaddamar da fara bincike kan wasu manyan jami'an sojin kasar, inda ake tsare da mutum daya da ya yi yunkurin tserewa daga Ukraine.
Ma'aikatar ta ce, manyan jami'anta da kuma shugabanin kamfanonin da ake siyan makamai sun yi yunkurin sama da fadi da dala miliyan 40 daga kasafin kudin makamai. Ma'aikatar ta kara da cewa, an sanya hannu kan kwantiragi da wani kamfani a watan Augutan shekarar 2022 da nufin samar mata da makaman artillery bayan an biya cikakken kudi, sai dai ba a aika wa Ukraine din makami ko guda daya ba.
Magance matsalar cin hanci da rashawa na daga cikin ka'idojin da Kungiyar Tarayyar Turai EU ta gindayawa Ukraine yayin da ta ke neman zama mamba.