1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta ce ta dakile hare-haren Rasha

January 1, 2023

Jiragen yaki 45 marasa matuka mallakin Rasha sun kai wa Ukraine hari a daren sabuwar shekara. Amma hukumomin Ukraine suka ce tuni dakarunsu suka yi nasraar cafke jirage 12 daga cikinsu.

https://p.dw.com/p/4LcMV
Ukraine ta zargi Rasha da kai mata hari da jirage maras matuka a KievHoto: Gleb Garanich/REUTERS

Rundunar sojin kasar Ukraine ta yi zargin cewa hare-haren na da hadin bakin kasar Iran da ke goya wa Rasha baya a wannan rikici, Iran ta saba samar wa Rasha da jiragen yankin da take yi wa Ukraine kutse da su. Sai dai duk da haka sojojin na Ukraine sun taya dakarunsu murnar shiga sabuwar shekara tare da karfafa musu gwiwar nasara.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da a gefe guda, Ukraine ta zargi Rasha da kai mata hare-hare da makamai masu linzami guda 20 a wannan Lahadi da ke zama ranar farko ta sabuwar shekara.