1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin kare kai a bangaren Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar
February 16, 2022

A wani mataki na hannunka mai sanda, Ukraine ta kaddamar da atisayen soji da nuna kishin kasa a daidai lokacin da shugabannin kasashen Turai ke gargadin Rasha.

https://p.dw.com/p/478TK
Ukraine Präsident Wolodymyr Selenskyj in Rivne
Hoto: AP/picture alliance

Shugaba Volodymyr Zelensky ya kasance a wurin da dakarun ke samun horo kan amfani da sabbin tankunan yaki da makamai da suka samu, a wani yanki da ke kusa da babban birnin kasar ta yammaci.

Sai dai rahotannin nuna karfin sojin Ukraine din ya sabawa hotunan kafafafen yada labaru, da ke nuni da cewar Rasha ta fara janye dakarunta da makamansu tare da kawo karshen atisayen sojojinta a yankin Crimea.

Har yanzu dai akwai fargaba a bangaren kasashen yammaci na Turai dangane da yiwuwar afkawa Ukraine din da yaki a bangaren Moscow ko wane lokaci.