1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta kai hari kan wata gada a Crimea

Mouhamadou Awal Balarabe
June 22, 2023

Wata gada da ta hade Crimea da yankin da sojojin Rasha suka mamaye ta lalace sakamakon harin da sojojin Ukraine suka kai a ci gaba da kai farmakin da suke yi.

https://p.dw.com/p/4SwcJ
Wannan gada ce ke hada Rasha da yankin crimeaHoto: Rosavtodor Press Office/TASS/IMAGO

Hukumomin Rasha da suka yi wannan shelar lalacewar gadar suka ce harin bai haifar da asarar rai ba, amma ana kan tantance irin barnar da aka yi. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi kasar Rasha da shirya wani harin da ya danganta da na ta'addanci da ka iya haifar da matsala a tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia. Sai dai Moscow ta yi tir da wannan zargi tana mai cewa karya ce tsagwararta.

Ita dai Ukraine ta jagoranci kai farmakin kwato yankunan da Rasha ta mamaye a kudanci da gabashin kasar. Amma dai fadar mulki ta kremlin ta ce wannan yunkuri na tafiyar hawainiya. Ya zuwa yanzu dai Ukraine ta ce ta kwace garuruwa takwas daga hannun Rasha cikin makonni uku.

A  wannan yanayi ne, shugabar gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi kira ga shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO da za su gana a Vilnius a watan Yuli, da su mai da hankali kan karfafa taimakon soji ga Ukraine.