1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta karyata ikirarin kwace garin Soledar

Ramatu Garba Baba
January 13, 2023

Gwamnatuin Kyiv ta karyata nasarar da Rasha ta ce ta samu na kwace iko da yankin Soledar mai albarkatun gishiri da ke a gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/4M9IF
Hoto: Valentin Sprinchak/TASS/picture alliance/dpa

Gwamnatin Ukraine ta karyata ikirarin Rasha na cewa ta kwace iko da garin Soledar, tana mai cewa, har yanzu tana da cikakken iko amma sun ci gaba da musayar wuta mai zafi, ta kara da jinjina wa sojojin kasar da suka tsaya kai da fata don ganin su kare martabar Ukraine.

Da safiyar wannan Jumma'a, gwamnatin Kremlin ta sanar da cewa, dakarunta sun karbe iko da garin nan Soledar da ke da albarkatun karkashin kasa na gishiri, Rasha ta ce, nasarar ce ta farko da take samu, bayan da ta shafe kusan watanni shida tana fuskantar koma baya a fadan da suke gwambazawa da makwabciyarta.

Kawo yanzu, ba a iya tabbatar da ikirarin Rashan ba a yayin da kasashen duniya musanman Amirka ke cewa, nasara kwace garin Soledar, ba wani abun a zo a gani ba ne, don kuwa ba za ta taba yin wani tasiri ba a kokarin Rasha na son yin galaba a kan Ukraine a yakin da ta kaddamar a watan Febrairun bara ba.