Ukraine ta koma bada iskar gas ga kasashen Turai
January 3, 2006Ukraine ta koma cikakken aikawa da iskar gas kamar yadda aka saba zuwa kasashen turai.
Wani memba na kamfanin Naftogas mallakar kasar,Mykola Goncharuk,yace a dai dai wannan lokaci kanfanin ya koma bakin aikinsa gadan gadan na tura iskar gas ga Kasashen Turai,inda yace a yau din nan sun tura cubic mita miliyan 360 zuwa kasashen na turai,wadda yace cika alkawari da suka dauka ne na samarwa kasashen iskar gas kamar yadda suka saba.
A wani labarin kuma kasar Austria da yanzu take rike da shugabancin KTT,tace ba zata matsawa Ukraine lamba ba game da rikicin iskar gas tsakaninta da Rasha,duk kuwa da wasika ta bukatar yin hakain da Rasha ta aika mata.
Kakakin gwamnatin Austria yace,kasarsa ba zata sa baki ko shiga tsakani cikin wannan batu ba, kamata yayi kakashen biyu su nemo bakin zaren warware wannan matsala tsakaninsu.