1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Ukraine ya kori wasu jakadun kasar a kasashe biyar

Suleiman Babayo AH
July 9, 2022

Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine ya fatattaki jakadun kasar a wasu kasashe biyar cikin har da Jamus daga bakin aiki.

https://p.dw.com/p/4DuFt
Ukraine | Präsident Selenskyj
Hoto: John Moore/Getty Images

Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine ya kori Andriy Melnyk jakadan kasar da ke Jamus daga bakin aiki, a wani kudirin doka da shugaban ya sanya hannu a kai. Sannan ya jakadun Ukraine a kasashe Norway, Jamhuriyar Czech, Hungari da Indiya duk an kore su daga bakin aiki.

Babu wani dalili da aka bayar kan matakin da shugaban kasar ya dauka, ko kuma makomar jakadun.

Shi dai Andriy Melnyk a matsayin jakadan Ukraine a Jamus ya yi fice wajen neman kayan yaki ga kasar domin mayar da martani bisa mamaya daga dakarun Rasha.