Ukraine ta kulla dangantaka da EU
March 21, 2014Yarjejeniya dai za ta yi sanadiyyar taimakwa Ukraine din yin garambawul na tsarin siyasarta da ma tattalin arziki, baya ga wani shiri na janye mata kudaden fito kan kayan da ta ke kerawa da za a yi da kuma wani tsari da aka fidda na bata tallafin kudi da yawansu zai iya kaiwa euro miliyan dubu 11 don farfado da tattalin arzikinta wanda ya ke tanga-tangal.
Nan gaba kuma a wannan shekarar ce kuma ake sa ran EU da Ukraine din za su sake sanya hannu kan wata yarjejeniya ta harkokin kasuwanci da kuma abin da ya danganci shari'a.
Shugaban majalisar zartarwa kungiyar ta EU Herman Van Rompuy ya ce wannan matakin da Ukraine din ta dauka ya nuna irin shaukin da mahukuntan kasar da al'ummarta ke da shi na ciyar da ita gaba.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe